Ɗan takarar zaɓen gwamnan Jihar Anambra Charles Soludo wanda ke gaba da ratar ƙuri’u 45,000, ya na daf da kafa tarihi idan ya lashe zaɓen ‘inkwankulisib’ da za a yi a wata ƙaramar hukuma, domin zama gwamna.
Soludo wanda tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) ne, zai kasance gwamnan CBN na biyu wanda ya taɓa zama gwamnan jiha bayan ya yi gwamnan babban bankin Najeriya.
Wanda ya fara yin gwamnan jiha bayan ya yi gwamnan CBN, shi ne Clement Isong, wanda ke jikin Naira 1000.
Isong ya yi Gwamnan Cross River tsakanin 1967 zuwa 1975. Ya sake zama gwamna dai a Cross River daga 1979 zuwa 1983.
Kuma tun bayan shi, har yau ba a sake samun wani ba, sai fa Charles Soludo, wanda a yanzu za a iya cewa ya jefa ƙafa ɗaya a gidan gwamnati, ƙafa ɗaya kuma na waje.
Charles Soludo wanda ya lashe ƙananan hukumomi 18 cikin 20 da aka bayyana sakamakon su, ya sha kaye a Ƙaramar Hukumar Ogbaru, inda can ne mahaifar Minista Stella Odua.
Sai dai kuma abin mamaki, ɗan takarar jam’iyyar PDP, Valentine Ozigbo ne ya kayar da shi, ba Andy Uba, ɗan takarar APC jam’iyyar su Stella ɗin ba.
Yayin da Ozigbo ya samu ƙuri’u 3,445, Soludo ya samu 3,051.
Tuni dai duk da kurin da Andy Uba yya riƙa yi, Soludo ya tsere masa fintinkau da ƙuri’a kusan 60,000.
Jihar Anambra ita ce jihar ta biyu wajen ƙankantar faɗin ƙasa a Najeriya.
Jihar Legas ce kaɗai ta fi jihar Anambra faɗi.
Discussion about this post