Jam’iyyar PDP ce ta lashe kujerar shugaban karamar hukumar Kajuru a zaben Kaduna da ka yi ranar Asabar.
Bayan haka PDP ce ta cinye kujerun kansiloli 9 APC mai mulki ta yi nasara a kujera ɗaya tal.
Da yake bayyana sakamakon zaɓen malamin zaɓe Ibrahim DanMaraya ya bayyana cewa Ibrahim Gajere na Jam’iyyar PDP ne yayi nasara a zaɓen da kuri’u 14,432, Cafra Caino na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 9,095.
Haka kuma PDP ce ta yi nasara a zaɓen kujerun kansiloli da aka yi.
Idan ba a manta ba Hukumar Zaɓe ta Jihar Kaduna ta ɗage zaɓen ƙananan hukumomi hudu saboda matsalar tsaro a zaɓen 4 ga wata.
Hukumar ta ɗage zuwa 25, wato Asabar din da ya gabata.