Yadda Munnir Sada ya rattaba hannu a yarjejeniyar shiga makarantar koyon buga kwallon ƙafa ta Arsenal – Jaafar Jaafar

0

Jaridu da dama sun wallafa labarin yadda kungiyar Arsenal ta ɗauki wani yaro ɗan shekara 8 a ƙungiyar.

Wannan yaro mai suna Munnir Sada yana taka leda ne a inda ake horas da yara ƙanana dake karkashin kungiyar Arsenal.

Fitaccen ɗan jarida, Jaafar Jaafar ya bi diddigin wannan labari inda ya tattauna kai tsaye da iyayen Munnir Sada don sanin ainihin abinda ake ciki game da wannan magana.

Jaafar ya ce ” Yanzu na gama magana da mahaifi da mahaifiyar Munir Sada, yaron da aka ce kungiyar wasan kwallon kafa ta Arsenal ta dauka.

Ga wasu muhimman batutuwa da na samu daga tattaunawar da mu ka yi.

1 – Shashen nemo yara masu nasibin kwallo ajin ’yan kasa da shekaru 10 ta “Arsenal Academy” ta zakulo Munir

2 – A watan Mayun wannan shekara ne su ka je da mahaifiyarsa aka masa rajista, duk da cewa ba makarantar kwana ba ce — zuwa su ke yi ‘training’ sau biyu zuwa uku a sati.

3 – Yaron shekarar sa takwas

4 – Kungiyar Arsenal ba ta bawa yaro ko mahaifan yaron da ke wannan mataki kudi don sun yi masa rajista.

Share.

game da Author