Warware Matsalolin Arewacin Najeriya Yana Bukatar Taron Dangi

0

Kasar Najeriya tana da yankuna guda biyu: Arewa da Kudu. Wad’annan yankunan suna da mutane masu yare da al’adu daban daban.

Tun bayan tafiyar turawan mulkin mallaka, ake samun cece-kuce a tsakanin bangarorin guda biyu. Hakan ya samo asali ne, kamar yadda wasu su ke gani, tun daga lokacin da Gwamna Luga (Lord Fredrick Lugard) ya hademu waje d’aya da sunan “Amalgamation”.

Arewacin Najeriya yana da nasibi, duk da makwabtanmu su na yi mana kallon marasa ilimi tun bayan mulkin mallaka, amma sai ga mulkin kasar Najeriya a hannunmu bayan tafiyar turawa. Menene ya kawo hakan? Jajircewa, kishi da hadin kai irin na su Sardauna da makamantansu. Wannan ne ya sa abokan zamanmu ‘yan kudu su ka hana mulkin zama lafiya a jamhuriya ta farko. Ka karantashi littafi mai suna “The Best Way To Survive In Nigeria” wanda M.K Soron Dinki ya rubuta.

To yanzu wani hali Arewa ta ke ciki? Mun fi kowa lalacewa yanzu saboda rashin kishi da hadin kai. An bar talauci da jahilci suna cin karensu ba babbaka a cikin al-umma. Wad’annan abubuwan guda biyu, tagwayen juna ne.

Kuma annoba ne ga kowacce al-umma. Sune su ka saka Arewa a halin da take ciki yanzu. Kuma idan har ba a yi musu da gaske ba, zasu kashemu da ranmu.

Abun mamaki, yanzu idan kana tafiya a mota. Idan ka fita daga Arewacin Najeriya sai ka samu nutsuwa saboda rashin tsaro. Wai kudancin Najeriya ta fi Arewa tsaro yanzu. A shekarun baya, idan za ka je Lagos.

Kuna shige Abuja za ka fara faduwar gaba, balle idan ku ka fara shiga kudu. To yanzu lissafin ya canza saboda sakacinmu gabad’aya. Mun koma kura-ta-ci-kura a tsakaninmu.

Arewan nan fa, ita ce yankin da Gwamna Luga, gwamnan mulkin mallaka mai wandon karfe ya yabeta a lokacin da yake gudanar da tsarin “Indirect Rule” saboda ya samemu cikin tsari da bin doka. Muna bin umarnin manyanmu. Ka karanta wancan littafin da na baka hujja da shi a farko.

To menene mafita? Tsarkin zuciya, addu’a da taron dangi. Dole ne sai kowa ya bada gudunmuwa. Shugabanni, malamai (Na addini da na boko), talakawa da kowa. Ana bukatar taron dangi don dawo da martabarmu da kwarjininmu na baya.

Gaskiya wannan ba Arewar da su Sardauna su ka bar amarta bace. An ci amanarsu. Allah ya jikansu da rahama.

Allah ya shiryar da mu.

Share.

game da Author