Gwamnati jihar Kaduna ta sassauta da dokar hana walwala a kananan hukumomin Kauru da Zangon Kataf

0

A ranar Asabar gwamnati jihar Kaduna ta sassauta dokar hana walwala da ta saka domin samar da zaman lafiya a kananan hukumomin Kauru da Zangon Kataf.

Kwamishinan tsaro da aiyukkan cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya sanar da haka a garin Kaduna.

Aruwan ya ce gwamnati ta sassauta dokar na awa 24 zuwa ayi walwala daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma a dalilin zaman lafiya da ya fara samuwa a kananan hukumomin.

Idan ba a manta ba Kwamandan rundunar sojjin dake aikin samar da Tsaro a wannan yanki, Kwamanda Okonkwo, ya shaida cewa babban matsalar da ake samu a wannan yanki shine ramuwar gayya.

Ya ce ” Wasu matasan ‘yan asalin Kataf sukan kai hari ga abokan gaban su wato makiyaya, haka kuma suma abokan gabar sukan dau fansa.

Gwamna Nasir El-Rufai ya kara da cewa gwamnati za ata cigaba da ganin an samu tabbatacciyar zaman lafiya a yankin da jihar baki daya.

Gwamna El-Rufai ya kara da cewa babban kandagarkin da zai wanzar da zaman lafiya a Kudancin Kaduna, shi ne kabilun da ke yankin su yi amanna da juna su zauna lafiya a tsakanin su, su daina kashe-kashen juna.

A dalilin rashin zaman lafiya da ake samu a yankin kudancin Kaduna, mafi yawa daga cikin mazauna yankin sukan kwana ne da ido daya a bude domin basu san me zai auku ba kafin safe.

Wannan ta’addanci da ake fama da shi, ba wannan yanki bane kawai abin yayi tsanani. Wannan hare-hare yayi tsanani a wasu yankunan jihar da dama.

Share.

game da Author