Gwamnati ta ware Naira biliyan 10 don inganta aiyukan noman rani

0

Kwamitin zantaswa na gwamnatin tarayya ta amince ta kara Naira biliyan 6.9 akan Naira biliyan 3.263 domin samun isassun kudaden kammala aiyukkan inganta noman rani da aka fara a Shonga jihar Kwara.

Ministan ruwa Suleiman Adamu ya sanar da haka wa manema labarai a Abuja bayan an tashi taron kwamitin.

Adamu yace an fara ayyukan inganta aiyukkan noma a Shonga tun a shekarar 2010 da Naira biliyan 3.263 domin kammala aikin amma sai aiki ya tsaya.

Ya ce ma’aikatar ruwa ta gano ci gaban da wannan aiki zai kawo wa kasa Najeriya idan da an kammla wannan hakan ya sa ma’aikatar ta dawo da maganar a taron kwamitin zantaswa ta kasa.

“ Mun kara yawan filin da za a yi amfani da su wajen noman rani daga hekta 1500 zuwa 2,300 sannan mun canja tsarin amfani da janareta zuwa amfani da na’uran wutan lantarki dake amfani da rana.

Ya ce wadannan canje-canjen da suka yi zai taimaka wa kasa wajen cimma burinta na inganta rayukan mutanen a kasar nan da hakan ya sa gwamnati ta kara Naira biliyan 6.9 akan ayyukan da za ayi.

Adamu yace za a kammala wannan ayyuka ne a cikin watanni 36.

Ya ce ma’aikatar ruwa za ta yi amfani da hekta 1.8 domin noman rani a kasar nan sannan tana shirin samun goyan bayan hukumomi masu zaman kansu domin a hada hannu a ga cewa an samu nasara akan wannan aiki da aka sa a gaba.

Share.

game da Author