Babban duniya ya tsara wasu aiyukan ci gaba guda shida da zai yi don inganta mutane a Najeriya.
Za a fara wadannan aiyuka ne a cikin wannan sheka, 2020, kuma bankin zai kashe dala biliyan 2.1885 wajen zantar da wadannan aiyuka.
Bankin ya ce aiyukan zasu taimaka wajen kawar da cin hanci da rashawa, inganta fannin kiwon lafiya, samar da aiyukan yi, inganta kasuwanci, Kauda talauci da dai sauran su a kasan.
Ga aiyukan guda shida
1. Inganta yi wa yara allurar rigakafi da inganta kiwon lafiyar mata.
Babban bankin zai bada karfi wajen ganin an maida hankali ga yi wa yara kanana musamman ‘yan kasa da shekara biyar rigakafin cututtuka da karfafa matakan kawar da zazzabin cizon sauro ta hanyar samar da gidajen sauro daga kashi 28 zuwa 41 bisa 100.
Za kuma a inganta aiyukkan cibiyoyin kuwon lafiya na matakin farko a wasu jihohi domin samar wa mata masu ciki kiwon lafiya kyauta.
Kungiya raya kasa da kasa ta (IDA) ce za ta dauki nauyin wadannan ayyuka sannan za ta kashe dala miliyan 650 a kai.
2. Inganta aiyukan noma a karkara da samar da kasuwan siyar da amfanin gona
Za a maida hankali ne wajen gina hanyoyi don jigilar kayan gona daga karkara domin sawwaka wa manona a lokacin da zasu rika fitar da amfanin gona a daka karkara zuwa kasuwanni.
IDA za ta bada dala miliyan 280, Hukumar samar da ci gaba na kasar Faransa za ta bada dala miliyan 230 sannan gwamnatin Najeriya za ta bada dala miliyan 65 domin samun nasara a wadannan ayyuka.
3. Katin dan kasa.
Banki zai tallafa wa hukumar yin katin dan kasa domin ganin an samu karuwar mutane masu yi nan da shekara uku masu zuwa.
Za kuma a tsaro hanyoyin da za su taimaka wajen karfafa gwiwar mazauna karkara da matasa wajen yin katin dan kasa.
IDA za ta bada dala miliyan 115 ,hukumar samar da ci gaba na kasar Faransa za ta bada dala miliyan 100 sannan bankin kasar Turai za ta bada dala miliyan 215 don samun nasarar wannan aiki.
4. Inganta tattalin arzikin jihar Ogun
Mara wa shirin horas da dalibai sana’o’in hannu a makarantun boko na mallakin gwamnati domin samun karin kashi 70 na daliban da za su iya ci da kansu da sana’ar hannun da suka koya.
IDA za ta bada dala miliyan 250 a wannan aiki.
5. Kirkiro hanyoyi da dabarun kwarewar aiyukka.
Burin wannan aiki shine inganta kwarewar aiyukan mutane 50,000 ‘yan Najeriya da kwarewar malaman makarantun koyar da fasaha yadda dalibai za su zama abin moriya ga kasa gaba daya.
IDA za ta kasha dala miliyan 200 domin ganin haka ya tabbata.
6. Ayyukan inganta muhalli
Za a inganta kwarewar mutane sama da 21,000 kan hanyoyin samar da ci gaban muhalli wanda suma za su taimaka wajen horas da mutane 4000.
IDA za ta bada dala miliyan 80 domin ganin hakan ya tabbata.
Discussion about this post