CORONAVIRUS: Babu dan Najeriyan da ya kamu da cutar a kasar Chana – Gwamnatin Chana

0

Gwamnatin kasar Chana ta bayyana cewa babu wani dan Najeriya dake kasar Chana da ya kamu da cutar.

Gwamnatin ta fadi haka ne a rahotan kullun da take yi game da matsayin cutar ga kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO).

Rahotan ya nuna cewa baki wadanda ke zama a kasar su 29 ne suka kamu da cutar inda daga ciki 18 sun warke, biyu sun mutu sannan tara na kwance a asibiti.

Daga cikinsu babu dan Najeriya ko daya.

Tun da wannan cuta ta bullo a lardin Hubei dake Wuhan a kasar Chana gwamnati take kokarin ganin ta dakile yaduwar cutar.

Hakan ya sa baki musamman ‘yan Najeriya dake zama a kasar yin kira ga gwamnati da ta kawo jirgin da zai kwashe su daga kasar.

Sai dai gwamnati Najeriya ta ce yin haka bashi da amfani.

A yanzu haka mutane 1076 ne ke dauke da cutar a kasashe 26 a duniya ban da kasar Chana.

Sannan a cikin awowi 24 kasar Iran ta rawaito cewa mutane biyar sun kamu da cutar inda daga ciki biyu sun mutu.

Duk da haka a kasar Chana gwamnatin ta ce ta samu raguwa game da yadda cutar ke yaduwa domin a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata adadin yawan mutanen da suka warke daga cutar sun fi adadin yawan da suke kamu da cutar.

Hukumar kiwon lafiya ta kasar Chana ta bayyana cewa mutane 74,576 ne ke dauke da cutar inda daga ciki 16,155 suka warke sannan 2,118 suka mutu a kasan.

Hukumar ta ce akwai sauran mutanen da suka kamu da cutar guda 4,922 a asibiti sannan an killace wasu mutane 126,363 da ake zargin za su iya kamuwa da cutar a dalilin kusantar wadanda suka kamu da cutar.

Daga nan dai WHO ta yi kira ga mutane musamman wadanda suka dawo daga kasar Chana da su killace kan su a gida na tsawon kwanaki 14 sun duba kansu domin gain ko sun kamu da cutar.

Ta ce a gaggauta zuwa asibiti a duk lokacin da mutum ya kamu da cutar domin yin haka na taimakawa wajen warkar da cutar a jikin mutum.

An bada lanbobbin wayar sallulan da za a iya kira da zaran an ga an kamu da cutar.

WHO ta ce har yanzu dai babu maganin cutar amma tana gudanar da bincike da kwararrun likitoci na duk fadin duniya gano maganin cutar.

Share.

game da Author