RIBAS: INEC ta ci gaba da tattara kuri’un zaben gwamna, bayan kotu ta kori karar neman hanawa

0

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta kori wata kara jam’iyyar AAC ta gabatar domin ta hana ci gaba da tattara kuri’un Jihar Ribas na Zaben Gwamna.

Kotun ta ce babu wata hujjar da jam’iyyar AAC za ta kafa da har za ta nemi a tsaida ci gaba da zaben da dokar kasa ce ta bada iznin aka gudanar da shi.

Mai Shari’a Inyang Ekwo ya zartas da hukunci cewa tunda dai abin da ake tankiya a kai, ya faru a baya, kuma a yanzu an shiga lokaci na bayan zabe, to Kotun Sauraren Kararrakin Zabe ce ta cancanta ta saurari karar da ita AAC din ta shigar, ba Babbar Kotun Tarayya ba.

Tuni dai a yau Talata INEC ta ci gaba da tattara sakamakon zaben, wanda ta ce bayan kammala tattarawa ne za a bayyana wanda ya yi nasara.

Sannan kuma AAC ta nemi a sake zabe a inda INEC ta ce an yi tashe-tashen hankulan da suka hargitsa zabe.

INEC ta ce idan har ta kasance zaben bai kammalu ba, sai an maimaita a wasu wurare ko rumfuna, to za a maimaita din a ranar 13 Ga Afrilu.

Share.

game da Author