Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta fitar da sanarwar dakatar da dukkan wasu ayyukan da suka shafi zabe a Jihar Ribas.
Wannan bayani ya na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da INEC ta fitar mai dauke da sa hannun Shugaban Wayar da Kan Jama’a da Yada Labarai na INEC na kasa, Festus Okoye.
INEC ta ce ta yanke shawarar dakatar da ayyukan ne saboda rahotannin da ta ke samu daga jihar Ribas na yawaitar tashe-tashen hankula da hargitsa zabe a wurare da dama a ranar da aka gudanar da zabe.
Ta kuma bada dalilai na yadda aka sace ma’aikatan INEC da hargitsa ofisoshin tattara sakamakon zabe da lalata takardun da ke dauke da alkalumman adadin wadanda suka jefa kuri’a da kuma lalata kuri’un su kan su.
INEC ta ce saboda kare lafiyar ma’aikatan ta da kuma kare kima da sahihancin zaben, ya zama dole ta dakatar da aikin zaben har sai wani lokacin da za ta yi sanarwa.
Ta ce za a kafa kwamitin bincike a gano dalilin da ya sa wasu da ba a ba su iznin kula kula da sakamakon zabe ba suka rika kwace sakamakon zabe ko kuma kekketa shi.