Gwamnatin jihar Kaduna ta nuna juyayin ta bisa harin da wasu mahara su kai kauyen Unguwan Barde dake karamar hukumar Kajuru, Jihar Kaduna.
Rahotanni sun bayyana cewa an kai wannan hari ne a safiyar Asabar inda wasu mahara suka fatattaki mazauna wannan kauye sannan suka rika cinna wa gidajen mutanen wuta.
Wani mazaunin kauyen da ya gudu ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa abin ya tada wa mutanen yankin hankali ganin cewa basu san hawa ba basu san sauka ba kawai suka ji ana banbanka wa gidajen su wuta.
A sanarwar yin jaje da Allah kyauta da gwamnatin jihar Kaduna ta fitar, wanda Samuel Aruwan ya saka wa hannu, ya roki mazauna wannan kauye da su hakura su zauna da juna lafiya sannan su gujewa daddako abin da zai tada zaune tsaye a yankunan.
” Bayannan kuma tuni gwamnati ta tura jami’an tsaro wannan yanki domin samar da dawwamammen zaman lafiya a jihar. Sannan kuma hukumar bada a gajin gaggawa ta garzaya wannan gari domin samar wa mutane kayan agaji a jihar.