Higuain ya rage wa Chelsea yawan firgita

0

Dan wasan Juventus wanda Chelsea ta saya daga hannun AC Milan, Gonzalo Higuain, ya ci kwallaye biyu a wasan Premier da ta buga da kungiyar Huddersfield Town a yau Asabar.

Higuian, wanda a makon da ya gabata ya fara buga wa Chelsea, kuma aka lallasa su da ci 4:0 a hannun Bournemouth, a yau ya wanke kan sa inda suka taka wasan da Chelsea ta yi nasara a gida da ci 5:0.

Higuain da Hazard su yi wasa sosai, ba kamar yadda a wasan su na baya suka hadu da samatsin kwallo ba.

Wannan nasara da Chelsea ta samu za ta rage wa kungiyar da magoya bayan ta, har ma da mai horaswa Mourizio Sarri karfin bugun zuciya, kasancewa wasanni da yawa a baya kungiyar ta kwance wa kanta zani a kasuwa.

A Kara Jamus kuwa kungiyar Brussia Dortmund ta kara yi wa Bayern Munich rata

Kungiyar kwallon kafa ta Brussia Dortmund da ke Jamus, ta kara bai wa babbar abokiyar adawar ta, Bayern Munch rata.

Dortmund dai ta yi kunnen doki 1:1 ita da Entracht Frankfurt. Hakan ya sa ta tsere wa Bayern da maki bakwai.

Ta na da maki 49, ita kuma Bayern na da 42.

Bayern ta sha kashi da ci 3:1 a hannun Bayern Leverkussen.

Share.

game da Author