Wolverhampton Wanderers ta je har gida ta lakada wa Everton ci 1-3

0

Kungiyar Wolverhampton Wanderers ta je har gida ta lakada wa Everton ci 1:3.

Dan wasa Raul Jimerez da Ruben Nevez da kuma Leander ne suka saka kwallaye a ragar Everton.

Andrea Gomez ya ci wa Everton kwallo daya tilo a ragar Wolves.

Sai dai kuma ana tsakiyar wasa sai wata murgujejiyar kyanwa baka kirin mai jajayen idanu ta keta ta tsakiyar filin.

Hakan ya sa alkalin wasa tsaida wasan cak, ana kokarin fitar da magen.

Magen dai ta keta fili daga farko har karshe duk da kokarin da masu hidimar aikin filin kwallon suka yi domin su fitar da ita.

Wani dan wasa ya ce shi jinin sa sam bai hadu da bakar mage ba.

“Ni a kasar mu a Belgium, aka alakanta bakar mage da alama ce ta rashin sa’a.”

Share.

game da Author