Buhari ya roki masana tarihi su tattara bayanan barnar PDP ta shekaru 16

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa akwai matukar muhimmanci masana tarihi da na tattalin arziki su tattara bayanan irin barnar da gwamnatin PDP ta yi a cikin shekaru 16, domin kada al’ummar da za ta zo nan gaba su maimaita irin wannan barnar.

Buhari ya yi wannan jamawbi ne a Fadar Gwamnati, a jiya Alhamis inda Kungiyar ‘Yan Takarar Shugaban Kasa suka kai maza ziyara. A ta su ziyarar dai sun ce sun ajiye muradin su na neman mulki, za su goyi bayan jam’iyyar APC ce.

Kakakin Shugaban Kasa, Femi Adesina ne ya bayyana labarin wannan taro da aka yi.

“Na yi murna da wannan irin kishi da ku ka nuna. Na san da kun so da kun hana ni kuri’un yankunan ku. Domin duk irin kaunar da jama’ar ku ke min, idan aka zo zabe, to a yankunan kun a san ku za su zaba.”

Amma Buhari ya ce ya ji dadi da ‘yan Najeriya suka fahimci muhimman matsaloli uku da ya sa a gaba, wato kawar da rashawa, matsalar tsaro da kuma inganta tattalin arziki.

Buhari ya shaida musu cewa an yi gagarimar asarar kudaden shiga a cikin shekaru 16 da PDP ta yi ta na mulki.

Ya tunatar da su yadda PDP ta bar titinan mota, hanyoyin jiragen kasa duk su ka lalace.

Ya ce da mulkin PDP ya gyara titina da sauran abubuwan da suka dace su yi, to da ‘yan Najeriya basu damu sosai ba. Kuma da ba su ma damu da ko wa ke shugabantar su ba.

“Ya kamata masana tarihin mu da masana tattalin arziki su tattara bayanan barnar da PDP ta yi a cikin shekaru 16, domin ‘yan baya su dauki darasi, yadda su ma ba za su mamaita irin abin da aka yi ba.

Shugaban Kungiyar mai suna Shittu Mohammed Kabir, wanda kuma shi ne daga jam’iyyar APDA, ya ce sun yanke shawara ne cewa ya kamata su goya wa Buhari baya saboda irin gagarimin ci gaban da ya samar a fannin tsaro, yaki da rashawa, samar da kayan more rayuwa, inganta harkar noma da sauran ci gaba a fannoni da dama.

Wadanda suka halarci ziyarar sun hada da: Edozie Madu, Independent Democrats; Danjuma Mohammed, Movement for Restoration & Defence of Democracy; Yusuf Nadabo Dantalle, Allied Peoples Movement; Ahmed Buhari, Save Nigeria Party; and Alhaji Isah B. Dansarki, Mass Movement of Nigeria.

Akwai kuma irin su: Ikechukwu Nwaokafor, Advance Congress of Democrats; Alista Soyode, Yes Party; Barrister Charles Ogbali, Advanced Nigeria Democratic Party; Kenneth Ibe Kalu, United Peoples Congress; Comrade Isiyaka Paul Femili, Nigeria Element Progressive Party; sai kuma Robinson Akpu, National Democratic Liberty Party.

Share.

game da Author