Ahirr Dinku Matan Arewa Akan Zaben 2019, Daga Mustapha Soron Dinki

0

Mata iyayen giji inji Bahaushe, idan babu ku babu gida. Gaskiya muna masu rokon ku da kuji tsoron Allah ku taimaka mana wajen samar da tubalin gina sabuwar Najeriya. Saboda kune bu ku damu da siyasa ba, kuma baku da ra’ayi akan wanda yakamata ku zaba a filin zabe.

Mafi yawancin ku kun dogara ne da abunda ‘women’s leader’ tace ku zaba saboda ‘dan abunda zata raba muku. Ku kyale woman’s leader a gefe, ‘yar kasuwa ce, dillancin ku take yi. A siyasa babu wata doka a cikin kundin tsarin mulki da tace wani ko wata ya baka zabi, wannan ma gidadanci ne kwarai da gaske.

Matan gida kun fi kowa sanin talauci domin kune ake barin ku da yara babu ko loma ‘daya a gida. Duk san da kuka zabi masu rauni akan za a baku dari biyu N200, to gaskiya idan abun yaje ya dawo kan ku yake dawo wa.

Kuna gani dai yadda ake sakin aure a Arewacin Najeriya, sannan ku duba yadda wasu daga cikinku suke zaman zawarci fiye da shekara takwas. Misali na kusa ma, ku duba yadda qannenku da yayinku suke zaune a gida babu miji.

Ku kuma matan Kiristoci tunda ba’a sakin ku sai dai a gudu a barku da yara ku mutu da wahala. Mafi rinjayen matsalar tana da alaka da rashin shugabanci na gari. Talauci yana cikin manyan matsalolin aure.

Ku duba fa ku ga yadda samari suke gudun aure ba wai don basa so ba sai don abun yafi karfinsu. Babu wanda zai qi aure saboda Shari’ar musulunci ne, nasan kuma babu mu’uminin da zai ki Shari’ar Allah. Muna so ku tsaya ku zabi mutanen kwarai a zabe mai zuwa. Ku kyale ‘women’s leader a gefe, idan kasa ta gyaru aure zamuyi mata itama ta huta da dillancin bata Najeriya. Idan aka samu gyara kune akan gaba wajen jin dadi saboda wani mawaki yace “komai na mata ne” Duk abun da maza suka samu kune kuke morarsa.

Don Allah ku tanadi katin zabe sai ku zama cikin shiri.

Allah yasa mu ga Alheri.

Share.

game da Author