KISAN KIYASHIN KAJURU: ‘Yan Sanda sun nesanta kan su daga adadin da El-Rufai ya sanar

0

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kaduna, Ahmad Abdurrahman, ya nesanta kan sa daga adadin mutanen da Gwamnan Jihar, Nasir El-Rufai ya ce an kashe a harin kisan-kiyashin Gidan Maro a Karamar Hukumar Kajuru.

Ya ce ‘yan sanda na ci gaba da bincike, kuma ba za su ambaci adadin da aka kashe ba, har sai sun kammala binciken su.

Sanarwar farko da El-Rufai ya yi a ranar 15 Ga Fabrairu, ya ce mutane 66 aka kashe a cikin rugage daban-daban na Fulani.

A cikin wata sanarwa kuma, bayan wanin taron sirri da Shugaba Muhammadu Buhari, El-Rufai ya ce wadanda aka kashen sun karu zuwa 130.
Dukkan sanarwar biyu da gwamnan ya yi dai sai da suka da ja-in-ja su ka biyo baya.

Shehu Sani, wanda shi ne sanatan da ke wakiltar yankin da rikicin ya barke, ya ce wadanda aka kashe ba su wuce 10 zuwa 15 ba. haka ya fadi bayan gwamnan ya yi sanarwar farko.

Wakilin PREMIUM TIMES da ya je yankin da rikicin ya barke, ya tambayi Kwamishinan ‘Yan Sanda karin bayani kan adadin da aka ce an kashe.
Bai shaida masa adadi ba, kuma bai jaddada adadin da gwamna ya ce an kashe ba. ya dai ce wancan adadi da shi gwamnan ya sanar, ba daga bakin hukumar ‘yan sandan jihar ya fito ba.

“A zaman yanzun idan gwamna ya ce maka mutum 200 ko kasa da haka ne aka kashe, to za sun iya kasancewa sama da haka kom kasa da haka.

Misali, akwai inda kuma ku ka je aka ce mana mutane 36 aka kashe. Da farko jami’an tsaro ba su shiga wurin ba, har sai da Fulani suka fito su na kuka bayan mun isa wurin tare da sojoji.

“Daga nan suka tunkari sojojin da suka yi mana rakiya, suka raka su rufe gawarwaki. Daga nan ne aka gano wadanda aka kashe a can.”

Kwamishinan ’Yan Sandan ya kara da cewa har yanzu jami’an sa na bincike, don haka ba zai iya tantance adadin da aka kashe ba, sai sun kammala tukunna.

“Kuma kamar yadda na fada wa gwamnan shi ma da kan sa, na ce, kisa irin wannan ba a saurin bayyana adadi tukunna, har sai an kammala bincike. Za ka iya cewa ga adadi a yanzu, an jima kuma ka sake cewa ga wani adadin. Har yanzu haka jami’an ‘yan sanda da na SEMA da SCO duk su na cikin dazuka su na bincike.

Ya ce dalili kenan ba su saurin bayyana adadi, har sai an kammala bincike tukunna.

Ya kuna ja kunnen cewa an gargadi mazauna yankin kada su sake su kawo wa binciken da ake yi kafar-ungulu.

Share.

game da Author