Magidanci ya roki kotu ta raba auren sa da matar sa saboda bin maza da take yi

0

Wani magidanci mai suna Taiwo Philip ya kai karar matarsa Bukola a kotun dake Bode Igbo dake Ibadan domin kotu ta raba auren su.

Philip ya bayyana a kotu cewa Bukola bata yi masa biyayya, bata kula da ‘ya’yan su, mafadaciya ce sannan tana bibiyan maza a waje.

” Ni dai sana’ar siyar da katako na ke yi a kasuwa sannan ina iya kokarina wajen ganin na kula da iyali na yadda ya kamata amma duk da haka matata bata da godiyar Allah.

” Wata rana na taba kama Bukola da wani tsoho a cikin shagon da na bude mata inda bayan na nemi sanin abin da tsohon yake yi a shagon wasu matasa suka taru suka yi mini dukan tsiya. Daga nan na kai kara a ofishin ‘yan sanda.

Philip ya roki kotu da ta raba auren sa da Bukola saboda ya gaji haka nan da auren.

Bayan haka Bukola ta amsa duk laifukan da Philip ya bayyana ta yi a kotun sannan ta roki alfarmar kotun da ta roki Philip ya yafe mata ya hakura kada a raba auren sai dai ita ma ta koka kan yadda ya yi mata a gida.

” Philip mafadacin mutum ne domin kulum sai ya ci zarafi na sannan baya dawo wa gida da wuri amma duk da haka na hakura na ci gaba da zama da shi.

A karshe alkalin kotun Muraina Agbomeji bayan ta kammala sauraren su ta daga shari’ar zuwa ranar 17 ga watan Disamba.

Share.

game da Author