Najeriya ta gode wa Switzerland saboda dawo da kudaden da aka wawura -Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya gode wa kasar Switzerland saboda sawo da kudaden da aka sata aka kimshe a kasar da ta yi zuwa Najeriya da kuma taimakon ta ga mutanen da zaman gudun hijira a sansanoni daban-daban a Arewa maso Kudu.

A cikin wata takardar manema labarai da Garba Shehu ya fitar a yau Talata daga fadar Shugaban Kasa, Buhari ya yi wannan godiyar bayan da ya karbi wasikar amincewa da kasar Switzerland ta aiko wa Buhari ta hannu Jakadan Kasar a Najeriya, George Steiner.

“Muna matukar godiya ga kasar Switzerland da ta amince aka dawo da makudan kudaden da aka wawura daga Najeriya aka kimshe a can kasar.

Ya kuma gode wa kasar saboda jajircewar ta wajen bayar da tallafi ga ‘yan gidun hijira masu zama a sansanonin gudun hijira da ke Arewa maso Gabacin kasar nan.

Daga nan sai Buhari ya jaddada cewa kyakkyawar hulda a tsakanin kasashen biyu za ta ci gaba da dorewa da kuma dawwama tare karfafa ta sosai.

Da ya ke nasa jawabin, jakadan ya sha alwashin cewa kasar sa za ta ci gaba da tallafa wa Najeriya musamman wajen ganin an magance babbar matsalar da ta addabi kasar, wato Boko Haram.

Ya kara da cewa kasar sa ta kuma sa-ido ta ga cewa an kara dankon dangantaka da cinikayya a tsakanin kasashen biyu.

Share.

game da Author