Kungiyar malaman Kwalejojin Kimiyya da Fasaha (ASUP) ta bayyana cewa tana nan kan bakarta na fara yajin aiki a duk kwalejojin kumiya da fasaha dake kasar nan.
Shugaban kungiyar Usman Dutse ya sanar da haka da yake hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Talata a Legas.
Dutse ya ce duk da cewa gwamnati ta gayyace su domin tattauna matsalolin da kwalejojin ke fama da su hakan ba zai sa su dakatar da shiga yajin aikin ba.
Idan ba a manta ba a ranar Larabar da ta gabata ne shugaban kungiyar malaman Kwalejojin Kimiyya da Fasaha (ASUP) Usman Dutse ya bayyana cewa malaman za su fara yajin aiki daga ranar 12 ga watan Disamba.
Dutse ya sanar da haka ne da yake ganawa da PREMIUM TIMES ta wayar tarho inda ya kara da cewa ASUP ta yanke shawarar haka ne saboda rashin biyan bukatun malaman da gwamnati ta ki yi.
Ya ce tun a shekarar 2014 ne kungiyar da gwamnati suka sa hannu a takardar yarjejeniyyar biyan bukatun malaman kwalejojin dake kasar nan amma shiru kamar ba ayi ba har yanzu.
” Mun gaji da kai ruwa rana tsakanin mu da gwamnati kawai mun yanke shawarar mu shiga yajin aikin kawai in ya so daga baya a san abin da da za yi nan gaba.