Humumomin Jami’ar Jihar Benuwai na binciken musabbabin sanadiyyar hana daliban jami’ar wadanda suka kammala karatun digirin farko na wannan shekara tafiya aikin bautar kasa da hukumar NYSC ta yi.
Shugaban Jami’ar ne, Msugh Kembe ya bayyana wa manema labarai haka a jiya Laraba.
Ya ce jami’ar ta yi mamaki kuma ta girgiza matuka jin cewa NYSC ta yanke hukuncin hana daliban jami’ar tafiya aikin bautar kasa a wannan shekarar.
“NYSC ba ta tuntubi jami’ar mu kafin ta yanke wannan hukunci ba. Sannan kuma ba ta sanar da mu cewa akwai tankiya a cikin jerin sunayen dalibai masu tafiya aikin bautar kasa a wannan shekarar na wannan jami’ar ba.”
Hukumar NYSC ta ce ta gano cewa an tsarma sunayen wadanda shekarun su sun haura ka’idar masu tafiya aikin bautar kasa, kuma an saka sunayen wadanda kwas din da suka yi ba za su tafi aikin yi wa kasa hidimar ba.
Haka Kodinetar NYSC ta jihar Benuwai, Awakessien ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai.
Ta ce fannin da ke kula da harkokin dalibai na jami’ar ya hada baki da wasu dalibai da dama wadanda bai dace su tafi aikin bautar kasa ba, amma aka saka sunayen su domin su je aikin ko ta halin kaka.
Ta kara da cewa an gano irin wannan harkalla a manyan makarantu shida a fadin kasar nan, wadanda yawancin su kuma duk daga jihar Benuwai suke.
Wannan hukunci kuma kamar yadda ta nanata, duk ya shafi sauran makarantun da suka jefa kan su cikin wannan harkalla, kuma duk an sanar da su.