Gidauniyar Dangote ta tallafa wa mata da naira miliyan 250 a Jihar Neja

0

Hamshakin attajiri Aliko Dangote, ya yi ganawar sirri tare da Tsohon Shugaban Kasa na mulkin soja, Ganar Ibrahim Babangida.

Su biyun dai sun gana a jiya Alhamis a katafaren gidan Babangida din da ke Minna, babban birnin jihar Neja.

Dangote ya kai ziyarar ce tare da ‘yar sa Halima, da kuma mijin ta Bello Suleiman, da kuma wasu ma’aikatan kamfanin Dangote.

Sun je Minna ne domin halartar taron raba kayan agaji na Naira milyan 250 da Gidauniyar Dangote ta raba wa mata masu karamin karfi har su dubu 25 a Minna.

Bayan kammala taron ne a dakin taro ne Dangote ya je wurin Babangida inda ya shafe awa daya a cikin gidan.

Bayan fitowar sa dai bai shaida wa manema labarai abin da suka tattauna ba.

Cikin wadanda suka take masa baya zuwa gidan Babangida har da Gwamnan Jihar, Abubakar Bello, Sanata Bala Ibn Na’Allah da Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dokokin Jiaha, Mikail Bmitosashi.

Share.

game da Author