Akwai yiwuwar masu kiba su zamanto mashaya taba sigari kamar yadda wani binciken kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO, ya nuna.
Wani babban masani kuma babban likita Paul Brennan ne ya fitar da sakamakon wannan bincike in da ya tabbatar cewa babu shakka akwai yiwuwar masu kiba za su afka wa shan taba sigari.
Yace kashi 70 bisa dari na kwayoyin halittar su ya nuna cewa lallai za su iya fadawa wannan harka.
Wannan bincike an buga shi ne a wata mujallar kasar Britaniya wanda hukumar gudanar da bincike kan cutar daji wato Kansa ta dauki nauyi.