TAMBAYA: Wace Aya ce mafi girma da daraja a Kur’ani?Tare da Imam Bello Mai-Iyali

0

AMSA:Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.

AYA MAFI GIRMAN DARAJA A AL-KUR’ANI

Ayar da tafi girman daraja a Al-Kur’ani it ace Ayatul Kursiyu, aya ta 255 a cikin sura ta 2: Suratul Baqara:

أعوذ بالله العظيم من الشيطان الرجيم
اللَّهُ لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ لَا تَأْخُذُهُ
سِنَةٌ وَلَا نَوْمٌ لَهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ
مَنْ ذَا الَّذِي يَشْفَعُ عِنْدَهُ إِلَّا بِإِذْنِهِ يَعْلَمُ مَا
بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ وَلَا يُحِيطُونَ بِشَيْءٍ مِنْ
عِلْمِهِ إِلَّا بِمَا شَاءَ وَسِعَ كُرْسِيُّهُ السَّمَاوَاتِ
وَالْأَرْضَ وَلَا يَئُودُهُ حِفْظُهُمَا وَهُوَ الْعَلِيُّ الْعَظِيم.

MA’ANAR AYATUL KURSIYU

Allah, babu wani Ubangiji face Shi, Rayayye, Mai tsayuwa da komai, gyangyadi baya kama Shi, kuma bacci baya kama Shi, Shi ne mai duk abinda yake cikin sammai da duk abinda ke cikin kasa, wane ne wanda yake yin ceto a wurin Sa, face da izinin Sa? Yana sanin abinda yake a gaba gare su da abinda yake abayan su, kuma ba su kewayewa da kome
daga ilimin Sa, face da abinda ya so. Kursiyyun Sa ya yalwaci sammai da kasa. Kuma tsare su baya nauyayar Sa. Kuma Shi ne madaukaki Mai girma. (Al-Baqara :255).

Wannan it ace ayar da tafi kowace aya girman daraja a cikin Al-Kur’ani. Ta kunshi tsantsar tauhidi da cikakken iko na Allah da tsananin girman Sa. Tana kunshe da sunayen Allah, da sunan Allah tafara kuma da shi ta kare.

KADAN DAGA CIKIN FA’IDOJIN AYATUL KURSIYYU

1. Ana samun sakamakon karanta ta a duniya cikin gaggawa, wato biyan bukata, kuma ga tarin lada gobe kiyama.

2. Ana karanta ta a kusurwowin gida hudu ko kusurwan daki don kariya daga shedanun aljanu da na mutane, kuma tana korar su daga cikin gida.

3. Duk wanda ya karanta ta a lokacin barcin sa, ko ya karantawa yaran sa Allah zai kare su har wayewan gari.

4. Ana karanta ta don kariya ga firgici da muyagun mafarkai.

5. Duk wanda yake karatun ayatul kursiyyu bayan sallolin farilla babu abinda zai hana shi shaga Aljanna sai mutuwa.

6. Ayatul kursiyyu na dauke da sunan Allah mafi Girma Ismullahil A’azam.

7. Duk wanda ya karanta ayatul kursiyyu da safe Allah zai tsare shi har yamma, kuma wanda ya karanta da yamma Allah zai kareshi har wayewar gari.

8. Lalle aya ce mai girma kuma za’a iya neman biyan bukata da ita ko neman waraka.

Allah ya biya bukata.

Share.

game da Author