Shugaban Darikar Cocin Angalika ya ziyarci Buhari

0

Shugaban Darikar Cicin Angalika na Duniya, Bishop Welbey ya ya ziyarci Shugaba Muhammadu Buhari A Gidan Abuja, na Landan, inda Buhari ke hutun murmurewa.

Dama dai Bishop din da kuma Buhari abokan juna ne da dadewa.

Mista Welbey ya ce ya yi matukar garin cikin ganin yadda Buhari ke murmurewa sosai. Har ma ya kara da cewa hakan wata hujja ce mai nuni da cewa Allah ya karbi addu’o’in da dimbin ‘yan Nijeriya su ka rika yi wa shugaban na su.

Shugaban na Angalika ya kuma jaddada cewa shi ma ba zai daina addu’ar da ya ke wa Nijeriya da shugaban na ta ba.

Da ya ke karbar gaisuwa, Shugaba Muhammadu Buhari ya gode wa Mista Welbey, wanda ya ce ya lura tsaye ya ke kyam wajen nuna damuwa a duk lokacin da ya ga ya shugaban na cikin wani mawuyacin hali.

Daga nan sai ya roki Allah da ya kara shige wa Welbey a gaba wajen jagorancin mabiya darikar sa na duniya.

Idan ba a manta ba, lokacin da tsohon Firayi Ministan Ingila David Cameron a wani taro a Landan ya ce ‘yan Nijeriya “maciya rashawa ne na musamman, a nan take sai Mr. Welbey ya nuna Buhari ya ce ” amma banda wannan bawan Allah din.”

Hakan dai ya faru ne a cikin 2016, a Landan.

Share.

game da Author