Sojin Najeriya zata ma ka PREMIUM TIMES a kotu saboda rubuce rubucen da tayi akan halin da sojojin Najeriya suka shiga a dajin Sambisa

0

Sojin Najeriya ta ce zata maka gidan jaridar PREMIUM TIMES a kotu saboda rubuce rubucen da tayi akan irin wahalhalolin da sojojin Najeriya suka shiga shiga a dajin Sambisa.

Wannan gidan Jarida ta rubuta labarai dauke da hotuna da bidiyo ya na nuna yadda sojojin Najeriya ke wahala a dajin Sambisa wanda ya hada da rashin ruwan sha, abinci, makamai da dai sauransu.

Manyan sojoji ne suka rasa rayukansu a yakin a dalilin ireiren sakacin da aka samu kamarsu ABU ALI da dai sauransu.
Sojojin basu ji dadin hakan ba inda suka ce zasu maka wannan gidan jarida a kotu domin hakan.

Shugaban wannan gidan jarida, Musikilu Mojeed ya ce zasu mika kukan sojin ga lauyoyin kamfanin sannan kuma ya ce kamfanin tana nan a matsayarta cewa ita ta rubuto wadannan rahoto.

Share.

game da Author