Sojin Najeriya ta sanar da gano gawawwakin sojojinta da suka bace makonni shida da suka wuce.
Lucky Irabor da ya sanar da hakan yace an gano gawawwakin sojojinne a bakin kogin Yobe.
Yace marigayi leftanar kanal K Yusuf na daya daga cikin wadanda suka rasa rayukansu a wannan harin da sojojin suka sha da ya kai ga bacewarsu.
Wannan gidan jarida PREMIUM TIMES ta bada wannan labari a wancan lokacin inda bayan musanta bacewar sojojin da sukayi inda daga baya hukumar sojin Kasa ta tabbatar da bacewar sannan ta kafa wata kwamiti domin ta binciki labarin in da ta gano cewa lallai wasu daga cikin mayakan sojin sun bace.
An binne su a makabartar barikin Maimalari.