Tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dattijai Ali Ndume ya ce abin da ya faru da shi zai iya fadawa kan kowa ma a majalisar.
“Abu daya da yayi mini dadi shine kowa ya sani cewa ban aikata wani laifi ba a majalisar aka cire ni.”
Bayan haka Ndume ya ce kamar yadda ya faru da shi haka zai iya faruwa da kowa ma a majalisar.
Ya kara da cewa babu abin da yayi mishi zafi kamar rashin tuntubar sa da ba’ayi ba akan koma menene yayi da yasa majalisar ta tsige shi.
” Sau 10 ina neman in sauka daga kujeran shugaban masu rinjaye a majalisar amma hakan bai yiwu ba.
Ya gode wa ‘yan uwansa sanatoci da irin goyon bayan da suka bashi lokacin da yake shugaban masu rinjaye a majalisar.
Discussion about this post