Shugabannin sojin Najeriya ‘yan wasan kwaikwayo ne kawai- Inji kanar TJ Abdullahi

0

Wani babban jami’in Sojin Najeriya kuma kwamandan rundunar soji na 151 dake banki Jihar Borno Leftanar Kanar TJ Abdullahi ya ce shugabannin sojin Najeriya su fito su gaya ma shugaban kasa Muhammadu Buhari gaskiya akan abinda ya ke faruwa da sojoji a filin daga musamman a jihar Borno.

TJ Abdullahi babban abokin BU Umar ne Wanda Boko Haram suka kashe a wata hari kwanakin baya.

Ya ce abin da shugabannin sojin su keyi yadda kasan ana shirya wasan Kwaikwayon Nollywood.

Yace sojojin suna cikin matsanancin hali a filin daga na rashin abinci, ruwan sha da makaman arziki.

Kanar Abdullahi ya ce karfin hali ne kawai na sojin Najeriya amma in ba haka ba shugabannin sojin Najeriya suna abinda suka ga dama da su.

Ya ce ko kashe abokinsa BU Umar da akayi akwai tambaya akai. Ya ce shugabannin sojin na taimaka ma Boko Haram da makamai sannan ya zargi shugaban kasa da kin ganin an kawo karshen yakin.

Hukumar sojin Najeriya ta karyata duka abubuwan da Kanar Abdullahi yace a hirarsa da abokanansa Wanda yayi a shafin sadarwa na WhatsApp Wanda ya kunshi abokanansa sojoji.

Yanzu dai an cire Kanar Abdullahi daga shugabancin rundunar soji na 151 dake banki jihar Borno sannan an gurfanar dashi gabar kwamitin ladabtarwan sojin Najeriya domin fadin irin wadannan maganganu dayayi cewa ya Saba dokar sojin a matsayinsa na jami’i.

Share.

game da Author