Hadi 5 da masoya finafinan Kannywood baya wuce su

4

Masoya finafinan Kannywood sun gano wadansu hadi da idan har furodusosi sukayi a finafinansu ya kansa su siya fina finan ko ta halin kaka.

Ga hadin

1 – Ali Nuhu da Aina’u Ade –

Masoya finafinan Hausa suna ganin duk da Ali Nuhu ya na hawa fim da kowace ‘yar wasa, duk lokacin da ka ganshi a fim daya da Ainau Ade sai ka ga abinda zai burge ka akan su.

“ Yadda kasan da gaske suke komai, wallahi, Ba na taba Wuce wani fim idan har naga Aina’u Ade da Ali Nuhu na cikin fim din.” Inji Hawwa Sani

Kalli fim din da kishiyar Gida

2 – Adam Zango da Aisha Tsamiya –

Kamar yadda a finafina Hollywood akwai Adam Sandler da Drew Barrymore haka a kannywood akwai Adam Zango da Aisha Tsamiya.

Idan dai soyayya kake so ka gani mai cike da abin al’ajabi da burgewa,kalli duk wata fim da kaga Adam Zango da Aisha Tsamiya.

“ Ni fa har kwaikwayonsu na keyi a soyyayyata da saurayi na. Idan ka ga Adam da Tsamiya to hankalinka zai kwanta idan kar tsantsagwaran soyayya kake son gani.” Inji Hindatu Mohammed

Kalli, Zeenat, So da dai sauransu.

3 – Jamila Nagudu da Suleiman Bosho

Za ka sha dariya kuma ka ga rikici kalakala idan har biyun nan suka fito a fim daya.

“ Babu mai maganin Bosho in ba Jamila Nagudu bane sannan Ita ma haka. Ina matukar son ganin finafinansu tare.” Inji Nasiru Ali

Kalli Mai Amada da dai sauransu

4 – Sadi Sani Sadiq da Hafsat Idris –

Sadiq Sani da Hafsta Idris hadi ne mai kayatarwa. Ko da yake Sadiq Jarumin gaske yana hawa da kowace jaruma kuma ya nuna gwanintarsa dan kwanakin nan gama shi da Hafsat Idris yana mutukar burge masoyan sa da ita.

5 – Rabiu Rikadawa da Hadiza Mohammed

Ida har a iyaye kake so kaga kwarewa to ka kalli fim din da Rikadawa da Hadiza suka fito tare.

Masoya finafinan Hausa na yaba ma hadin wadannan jarumai a kowace fim ne.
Kalli Adon Gari.

Share.

game da Author