Kakakin shugaban Kasa Garba Shehu da babban mai ba shugaban kasa shawara akan harkar watsa labarai Femi Adeshina sun musanta rade-radin da ake ta yadawa a shafunan sadarwa na yanar gizo cewa wai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rasu.
Garba Shehu ya ce shugaban na nan cikin koshin lafiya a kasar Ingila inda ya tafi hutu.
Sun yi Kira ga masu yada irin wannan jita-jita da su dai.