Kungiyar gwamnonin arewa ta sanar da cewa za ta hada kai da gwamnatoci da masu fada aji a yankin domin ganin an samu zaman lafiya mai dorewa da tsaro a iyakokin kasa Najeriya.
Shugaban Kungiyar gwamnonin Arewa Kashim Shattima yace za su tabbatar da ganin cewa sun yi wa duk wani Fulani makiyayi da ba dan kasa Najeriya ba ne rijista domin sanin zirga-zirgarsa a ko ina a yankin.
Yace hakan zai rage matsalar da ake fama dashi musamman akan zargin hare-haren da akeyi wa Fulani makiyayan.
Ya fadi hakan ne a taron da gwamnonin su ke yi a jihar Kaduna.
Ya kuma ce dole ne ‘yan Najeriya su ba harkar tsaro matukar kula saboda hakan ne kadai zai sa kasar ta samu cigaba mai amfani.
Ya yi bayani akan yadda kungiyar take kokari ta ga cewa duk wani dan Najeriya zai iya zama a duk inda ya ke so ba tare da an muzguna masa ba ko kuma an nuna masa wariya na asali.
Kashim Shettima ya bada misalin gwamnonin jihar Kano wanda aba asalin ‘yan jihar bane kuma sukayi gwamna a jihar.
Sabo Bakin Zawo dan asalin jihar Neja ne amma har gwamna yayi a jihar Kano, haka Ibrahim Shekarau dan asalin jihar Borno ne shima sai da yayi gwamnan a jihar.