Jami’ar Umaru Musa ba ta ce za ta hana rijistar wata kungiya ba – Inji Shugaban Jami’ar

0

Shugaban Jami’ar Umaru Musa da ke jihar Katsina Idris Funtua yace babu wani shiri da jami’ar ta yi akan hana wata kungiya gudanar da ayyuakanta a jami’ar musamman idan tana da rijista.

Yace gidan Jaridu ne suka lankwasa sanarwan da jami’ar tayi akan kungiyoyi da ya hada da na addini.

Shugaban Jami’ar yace abinda ya sa aka ce babu wata kungiya da zata gudanar da ayyukanta a jami’ar idan ba na MSS bane shine domin a rage yawan kananan kungiyoyi da suke fitowa da sunan kungiyoyin mususlunci gudun kada a sami rudani akan hakan.

Yace duk wata kungiya da ta shafi addinin musulunci za tayi rijistane a karkashin kungiyar dalibai musulmai MSS wanda hukumar jami’ar ta sani kuma ta yarda da ayyuakanta.

Ya yi kira ga mutane da su yi watsi da wannan magana domin ba haka bane.

Share.

game da Author