Wata kotu a jihar Kano ta gurfanar da wadansu magidanta masu suna Babangida Ubale da Isyaku Musa ‘yan asalin karamar hukumar Bici da laifin aikata fyade akan wadansu kananan ‘yan mata masu talla.
Kamar yadda mai shigar da kara ya fadi, Babangida da isiyaku sun rudi ‘yan matanne cewa za su siya kayansu sai suka kule da su wani gida suka cire musu kamfai kuma sukayi musu fyade.
Babangida da Isiyaku sun ba yaran kyautar naira 100 bayan sun gama.