Dokar hana ayyukan kungiyoyi a jami’ar Umaru Musa, musulmai ne zai shafa ba kiristoci ba

0

Hukumar jami’ar Umaru Musa dake Katsina ta musanta korafe-korafen da ake tayi akan cewa wai soke ayyukan kungiyoyi da hukumar jami’ar tayi zai shafi har da kungiyar Kiristoci na jami’ar ba haka bane.

Shugaba mai kula da ayyuakn dalibai a jami’ar Suleiman Kankara yace babu wata kungiya a jami’ar da akayi mata rijista da sunan kungiyar dalibai Kiristoci wato (Christain Student Association) a jami’ar.

Yace dalilin kafa dokar shine domin a dakatar da wadansu kananan kungiyoyi da suke kokarin bullowa a jami’ar kuma suke da alaka da akidun addinin musulunci da bam da bam, Kamar su kungiyar dalibai mabiya akidar Darikar Tijjaniyya, da dai sauransu.

“ Kungiyar Dalibai Musulmai (MSS) ne kawai muka sani kuma za mu bari”.

Yace har yanzu da yake Magana ba’a kawo gabansa wata kungiya ba don neman rijista da ya shafi dalibai mabiya addinin kirista ballantana ace wai jami’ar ta hana.

Daga karshe Suleiman kankara yace dokar zai shafi musulmai ne kuma anyi ne domin a guje ma barkewar wata matsalar da zai sa jami’ar tayi da ta sani nan gaba.

Share.

game da Author