Korona ta sa an sake saka dokar hana zirga-zirga a Jihar Bayelsa

0

Gwamnatin jihar Bayelsa ta saka dokar hana zirga-zirga a jihar domin dakile yaduwar sabuwar nau’in cutar Korona da ta bullo a jihar.

Bisa ga sanawar gwamnati dokar zai fara aiki ranar 15 ga Mayu daga karfe 8 na dare zuwa 6 na safe.

Kwamishinan yada labarai na jihar Chief Ayibaina Duba ya sanar da haka ranar Juma’a a wata takarda da aka raba wa manema labarai a garin Yenagoa.

Duba ya ce gwamnati ta yi haka ne domin kare mutane a jihar da kamuwa da cutar.

Ya ce gwamnati za ta saka jami’an tsaro domin ganin mutane sun kiyaye dokar a jihar.

“A dalilin haka duk wasu hanyoyin shiga jihar da suka hada da iyakan dake tsakanin jihohin Bayelsa/Delta dake Adagbabiri, Igbogene da iyakan dake tsakanin jihohin Bayelsa/Rivers dake Mbiama za za a rufe su.

Ya yi kira ga mutane da su kiyaye dokar hana walwala da gwamnati ta saka domin jami’an tsaro ba za su yi kasa-kasa ba wajen hukunta duk wanda ya karya dokar.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Juma’a ya nuna cewa mutum 49 sun kamu da cutar korona a kasar nan.

Hukumar ta kuma sanar cewa an gano wadannan mutane a jihohi 5 a kasar nan.

Enugu 22, Lagos18, Rivers 6, Akwa Ibom 2 da Edo 1.

Tun bayan bullowar cutar gwamnati ta yi wa akalla mutum 1,977,479 gwajin cutara kasar nan.

Zuwa yanzu mutum 165,661 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 156,399 sun warke, 2,066 sun rasu.

Mutum 7,196 na killace a asibiti.

Share.

game da Author