Gwamnoni su fara rufe tsiraicin da su ka yi wa jihohin su, kafin su nemi sutura a hannun Gwamnatin Buhari -Sanata Lawan

0

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya ja hankalin gwamnonin Najeriya da sauran masu rike da mukaman siyasa cewa bai kamata a ce irin su ne ke shiga sahun gaba wajen raji, karaja da tayar da jijiyoyin wuya wajen neman ballewa daga Najeriya ko kiraye-kirayen sauya fasalin kasa ba.

Lawan ya yi wannan gargadin a lokacin ganawa da manema labarai bayan ya kai gaisuwar Sallah ga Shugaba Buhari, tare da Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila.

Shugaban na Majalisar Dattawa ya ce, “ba wai cewa na yi masu wsdannan kiraye-kiraye su na da laifi ba. Amma dai ba daidai ba ne a ce gwamna da kan sa ko wani mai rike da babban mukamin siyasa ya rika fitowa ya na hauragiyar sauya fasali ko neman ballewa daga Najeriya ba.

“Idan ka na gwamna, to ya kasance ka fara sauya fasalin jihar ka ta hanyar yi wa kowane bangare na al’ummar jihar adalci, kafin ka fito neman gwamnatin tarayya ta sauya fasalin ikon kasa tukunna.

“Na san akwai bukatun da ake kiraye-kirayen a aiwatar wadanda tsakani da Allah da gaskiya ake neman a biya su. Amma idan gwamna ya ki aiwatar da adalcin raba-daidai a jihar sa, me kuma zai sa ya fito ya na tayar da jijiyoyin wuya kan a sauya fasalin kasa?”

Lawan ya hore su da cewa masu rike da mukamai su guji furta kalaman da ke hassara rudani a cikin kasar nan.

A na sa jawabin, Gbajabiamila ya ce matsalar da ta dabaibaye Najeriya a yanzu, ba laifin mutum daya ba ne.

Ya ce kowa na da na sa laifi a kasar nan.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda Kudirorin Gwamnonin Kudu 17 sun fusata Osita Shugaban VON, ya cumuimuyi Gwamnonin Najeriya 36 ya watsa bola.

A wankin babbanbargon da Shugaban Muryar Najeriya (VON), Osita Okechukwu ya yi wa Gwamnonin Kudu 17 wankin babban bargo bayan sun fitar da kudirori 12, wadanda a cikin su har su ka haramta kiwon shanu kuma su ka nemi a kyale jihohi su kafa ‘yan sandan su, kuma a gaggauta sauya fasalin Najeriya.

Tare da ragargazar gwamnonin, Osita ya hada gaba dayan gwamnonin Najeriya ya yi masu kwasar-karan-mahaukaciya ya watsa su cikin bola.

Ya bayyana cewa matsawar Najeriya ta yi mummunan sakacin da ta kara wa gwamnoni karfin iko, to sai kuwa an yi mummunan da-na-sani nan gaba ba da dadewa ba.

“Shin a yanzu ma wace aka cika, irin yadda gwamnoni su ka zama Fir’aunonin kan su, su na take doka yadda su ka ga dama, to ina ga an kara masu karfin iko kuma?

“In banda rashin kunya, gwamnonin nan fa tun cikin 2018 Shugaba Muhammadu Buhari ya sa wa dokar cin gashin kan kotunan jihohi da Majalisar Dokokin Jihohi. Amma har yau gwamnonin Najeriya sun shafa wa idanun su toka, sun ki fara aiki da dokar.

‘Yanzu irin wadannan Fir’aunonin da ke take doka sun hana kotuna da Majalisar Dokoki cin gashin kai, su ne za su nemi a ba su dama su kafa ‘yan sandan jihohi? Ya ku ke tsammani za ta kasance kan ‘yan adawa idan irin su Gwamna El-Rufai da Gwamna Wike su ka kafa ‘yan sandan kan su a jihohin su?”

Osita ya ce tabbas daga cikin korafe-korafen da gwamnonin su ka yi, akwai abin dubawa. To sai dai bai goyi bayan a kara wa gwamnonin jihohi wasu karfin iko fiye da wanda gare su a yanzu ba. Na yanzu din ma ya yo masu yawa, kuma sun fi kowa take doka.

“Gwamnonin da kuma ke tayar da jijiyoyin wuya kan sake fasalin Najeriya, tunanin su kawai su kara samun kudin shiga. Ka ji tashin-ta-ido. Wai mutanen da su ka hana Majalisar Dokoki ta Jihohi da kotunan jihohin kasar nan cin gashin kai a rika ba su kudaden su kai-tsaye daga tarayya, su ke neman karin kudade kuma.”

Osita ya ce kudaden da ake ba su din ma yanzu ai me za su iya tinkahon sun yi da su don amfana wa jama’ar jihohin su?

Osita ya nemi duk dokar da ta shafi ‘yan Najeriya baki daya, to ta kasance dokar tarayya ce ta kasa gaba daya, don kada wasu tsirarun jihohi su rika kakaba dokar da za ta zamo wa kasar nan jangwangwama daga baya.

Ya na magana ne kan kudirin haramta kiwo sasakai da gwamnonin kudu 17 su ka kakaba a jihohin su.

Share.

game da Author