Dan sandan da ya maida naira miliyan 1.2 da ya tsinta a wurin a hadarin mota ya samu kyautar naira 100,000

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa daya daga cikin ma’aikacin ta mai suna sajan Kabiru Isah ya maida wa ‘yan uwan wani mutum da ya rasu a hadarin mota tsabar kudi har naira miliyan 1.2.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar Abdullahi Haruna ya sanar da haka ranar Asabar a garin Kano.

Haruna ya ce Isah ya tsinci naira miliyan 1,294,200 a wurin da aka yi hadarin mota.

” Hadarin ya auku ne a hanyar Kaduna zuwa Kano inda wani mai mota ya banke wani mutum a bisa babur kuma nan take ya mutu.

Shi wannan dake kan babur di a she akwatin da yake dauke da ita kudi ne makil a ciki.

Haruna ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Sama’ila Dikko wanda ya mika wa ‘yan uwan mamacin kudin ya yi kira ga ‘yan sanda da su dauki darasi daga da abin kirkin da Isah ya yi a aikin sa. Yana mai cewa Isah ya nuna jarumta da kishin kasa da gaiskiya a aikin sa.

Bayan haka shugaban hukumar kula da kiyaye dokokin hanya na jihar Kano Baffa Dan-Agundi ya yi wa Isah kyautar Naira 100,000 a dalilin gaskiya da ya nuna a aikinsa.

Rundunar ta kuma tallafa wa mata zaurawa da mazansu ‘yan sanda suka rasu guda 26 da kayan abinci da sutura.

Share.

game da Author