Hukumar Gudanarwar Jami’ar East Carolina ta ce duk da ta na tausar zuciyar Gwamna Abdullahi na Jihar Kano, a kan zubar masa da kimar da Dakta Mbarika ya yi, gwamnatin jihar ba ta da hurumin umartar jami’ar ta ECU yadda za ta hukunta wanda ya ba shi kyautar farfesa a madadin jami’ar ba bisa ka’ida ba.
Cikin wata wasika da jaridar The NATION ta buga wa ECU a matsayin talla a ranar 8 Ga Disamba, 2020, kuma Mista Hayes ya sa hamnu, ya ce jami’ar ba ta ji dadin abin da aka yi wa Ganduje ba.
Ya kuma nanata cewa ba da yawun jami’ar Dakta Victor Mbarika ya yi wa Ganduje kyautar ‘farfesa’ da gayyata koyarwa a jami’ar ba.
“Kuma Gwamnatin Jihar Kano ta sani cewa Babi na 126 na Dokar Jami’ar ECU ba ta bada hurumin ta hukunta wani daga cikin malaman ta ko ma’aikatan ta don ya yi laifi a hukunta shi a bainar jama’a ba.
PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa Gwammatin Kano na so jami’ar Amurka ta nemi afuwar Ganduje
Gwamnatin Jihar Kano ta nemi jami’ar Amurka ta bada hakuri ga Gwamna Abdullahi Ganduje, bisa rikita-rikitar kwatagwalcin da ya biyo bayan ‘daukar Ganduje’ ya rika koyarwa da aka yi, amma daga baya jami’ar ta karyata.
An nemi Jami’ar East Carolina ta bada hakurin sannan kuma ta hukunta wani malami a jami’ar mai suna Victor Mbarika, wanda shi ne na ya sanar da Ganduje daukar sa aikin koyarwar, wanda iami’ar ta ECU ta karyata, ta ce hukumar jami’ar ha ta da wata akala ta kusa ko ta nesa da Ganduje.
Gidan Gwamnatin Kano ya ce a ranar 30 Ga Nuwamba ne Mbarika ya gabatar wa Ganduje da albishir din daukar sa aikin koyarwar na jifa-jifa.
PREMIUM TIMES ta yi mamakin yadda har jami’ar East American University za ta dauki Ganduje, gogarman da aka nuno shi ya na danna milyoyin daloli cikin manyan aljifai, a cikin 2018.
Da wakilin mu ya tuntubi jami’ar, don jin yadda ta yi mu’amala da Ganduje, gogarman danna dala cikin aljihu, sai mahukuntar jami’ar su ka ce ba su gayyaci Ganduje ba.
Baya ga karyata Ganduje da jama’ar ECU ta yi, ta kuma turo wa PREMIUM TIMES wasikar tabbacin karyata ta shi din da jami’ar ya yi.
Kuma ita din ce su ka aika wa Ganduje, su ka sanar da shi cewa, takardar gayyatar da Farfesa Victor Mbarika ya bai wa Ganduje, to ba ta wani bambanci da takardar tsire ko ta balangu.
Borin-kunyar Ganduje: Ganin yadda ‘yan Najeriya su ka rika caccakar Ganduje, sai ya fusata ya aika wa jami’ar wasika, ya nemi ta hukunta Mbarika, wanda ya shirya wa Ganduje gadar-zare, shi kuma ya rufta.
Sakataren Gwamnatin Kano, Usman Alhaji, wanda ya rubuta wasikar, ya jaddada cewa Ganduje bai roki a ba shi aikin koyarwar ba, kuma ba saye ya yi da kudi ba.