Darektan yada labarai na hukumar gidajen yari, Mohammed Manga ya bayyana haka ranar Talata.
Manga yace ” Gidajen yari biyu masu Zanga-Zangar #EndSARS suka fasa, bayan sallamar fursinonin da suka yi sun fasa dakin ajiye makama sun yi awon gaba da su.
” Dagangar suka aikata haka domin su zo cikin shiri ne.
Baya ga fasa gidan kurkuku, an shiga Babbar Kotun Edo ta 4, aka lalata wani sashe na ta, sannan kuma aka yi awon-gaba da wasu ababen da ke cikin kotun.
Dama tun misalin karfe 7 na safe hasalallun su ka yi dafifi a kan Titin Sapele, su ka rika cinna wa tayoyi wuta, tare da maida masu motoci komawa baya.
Sun afka wa kurkukun yayin da su ka kara yawa sosai. Sun fasa wani sashe na dogon bangon kurkukun, inda wasu kuma su ka yi kumumuwar-shahadar-kuda, su ka taka bango da waya, su ka dira cikin kurkukun.
Wasu daurarrun sun gudu da harbin bindiga a jikin su, yayin da wani dattijo da ya fito aka kama shi, lokacin da aka farga ya na tafiya tamkar wanda ke bi ya na wucewa a gefen hanya.
Dokar Ta-baci: Gwamnatin Edo ta kafa dokar hana zirga-zirga tsawon awa 24, inda aka bada umarnin cewa daga karfe 4 na yamma ba a son ganin kowa a waje.
“Wannan doka ta zama tilas. Yayin da Gwamnatin Jihar Edo ke mutunta ‘yancan yin zanga-zangar lumana, to kuma ba za ta zuba ido wasu bayagari su tashi hankalin jama’a ba.
“Makarantu da wuraren hada-hadar kasuwanci su kasance a kulle, har zuwa lokcin da za a ji wani karin bayani daga bakin gwamnati.”
Discussion about this post