Gwamnatin Jihar Edo ta bayyana cewa babu rana ko lokaci tukunna da za a ce za a fara janye dokar-ta-bacin awa 24 da aka kakaba a jihar.
An sa dokar ne a ranar Litinin, bayan da wasu batagari su ka shiga cikin rigar zanga-zangar #EndSARS, su ka fasa kurkukun Benin, kuma su ka kone ofishin ‘yan sanda biyar a babban birnin jihar.
Har yau dai ba a tantance yawa da adadin daurarrun da su ke tsere daga kurkukun ba, amma dai mahukunta sun ce ana kan bincike.
Gwamnati ta shawarci dukkan dalibai su ci gaba da zama a gida. Kuma ta ja hankalin iyayen yara cewa kowa ya tsare yaron sa a gida.
Ta ce an bai wa jami’an tsaro dama kama duk wani wanda ya karya dokar hana karakaina, kuma za a hukunta shi.
Tun a ranar Litinin PREMIUM TIMES HAUSA ta ruwaito cewa an kafa dokar-ta-baci a Edo, bayan masu zanga-zanga sun fara kirkuku sun saki fursunoni.
Zanga-zangar #EndSARS ta koma tarzoma a Jihar Edo, yayin da masu zanga-zanga su ka fasa gidan kuskuku su ka saki fursunoni a Babban Kurkukun Benin.
Wannan ya tilasta wa Gwamna Godwin Obaseki na Edo kafa dokar-ta-baci tsawon awa 24, domin kokarin shawo kan lamarin.
PREMIUM TIMES ta gano cewa matasa ne su ka karbe ragamar zanga-zangar su ka kutsa su ka saki wasu daurarrun cikin kurkukun.
Matasan wadanda sun kai 100, wasun su day yawa sun samu raunuka ya yin da su ka yi arangama da artabu tsakanin su day jami’an tsaron kurkukun, wadanda aka ce sun rika harba bindigogi.
An Lalata Babbar Kotu
Baya ga fasa gidan kurkuku, an shiga Babbar Kotun Edo ta 4, aka lalata wani sashe na ta, sannan kuma aka yi awon-gaba da wasu ababen da ke cikin kotun.
Dama tun misalin karfe 7 na safe hasalallun su ka yi dafifi a kan Titin Sapele, su ka rika cinna wa tayoyi wuta, tare da maida masu motoci komawa baya.
Sun afka wa kurkukun yayin da su ka kara yawa sosai. Sun fasa wani sashe na dogon bangon kurkukun, inda wasu kuma su ka yi kumumuwar-shahadar-kuda, su ka taka bango da waya, su ka dira cikin kurkukun.
Wasu daurarrun sun gudu da harbin bindiga a jikin su, yayin da wani dattijo da ya fito aka kama shi, lokacin da aka farga ya na tafiya tamkar wanda ke bi ya na wucewa a gefen hanya.
Dokar Ta-baci: Gwamnatin Edo ta kafa dokar hana zirga-zirga tsawon awa 24, inda aka bada umarnin cewa daga karfe 4 na yamma ba a son ganin kowa a waje.
“Wannan doka ta zama tilas. Yayin da Gwamnatin Jihar Edo ke mutunta ‘yancan yin zanga-zangar lumana, to kuma ba za ta zuba ido wasu bayagari su tashi hankalin jama’a ba.
“Makarantu da wuraren hada-hadar kasuwanci su kasance a kulle, har zuwa lokcin da za a ji wani karin bayani daga bakin gwamnati.”
Discussion about this post