Gaskiyar Da Wasu Ke Gudu Daga Gareta Ta Bayyana, Daga Imam Murtadha Gusau

0

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Assalamu Alaikum

‘Yan uwa bayin Allah masu daraja, Allah shine shaida, na dade ina bayyanawa mutane cewa, maganar gutsutsura masarautar Kano mai daraja da cin mutuncinta da gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje yayi, wallahi ba domin ci gaban jihar Kano da Kanawa ba ne, kuma yayi shi ne ba don wani alkhairi ga Kano da Kanawa ba, a’a, yayi shi ne kawai don ya musgunawa Mai Martaba Malam Muhammadu Sanusi II. A wancan lokacin da nike fadin wannan maganar, sai aka samu wasu ‘yan tsiraru, jahilai, wadanda basu fahimci komai ba, suna cewa wai an yi ne da zuciya daya, wai anyi ne domin ci gaban jihar Kano.

Sai ga shi kwatsam, an wayi gari wai yau, dokar nan da gwamna Ganduje yasa ‘yan amshin shatar sa, wato ‘yan majalisar Jihar Kano suka yi a can baya, domin a ci mutuncin Sarki Sanusi II, dokar da ke cewa za’a yi karba-karba duk bayan shekara biyu, na jagorancin shugabancin majalisar sarakuna ta Jihar Kano tsakanin sarakuna biyar, wato na Kano, Bichi, Gaya, Karaye da Rano, to yanzu ana so kuma a soke wannan doka, domin Aminu Ado ya zama shugaban majalisar sarakunan jihar Kano na dindindin. Wato jama’ah kun ga anan, hatta ma sauran sarakunan guda hudu, Ganduje ya yaudare su, ya ha’ince su. Domin basu taba tsammanin zai yi masu haka ba. Ai kadan ma kenan suka fara gani, da ma malam bahaushe yace, ‘MUNAFUNCI DODO NE, YA KAN CI MAI SHI’!

Anan sai in ce Alhamdulillahi, mun gode Allah, domin yanzu dai ya bayyana a fili karara, duniya ta amince kuma ta shaida cewa, duk makirce-makirce, da kulle-kulle da aka yi ta yi, anyi ne domin a musgunawa mutun daya, wato shine Sarki Muhammadu Sanusi II. Kuma duk wannan ana yi masa ne ba domin komai ba sai saboda hassadar shi da suke yi game da irin dimbin baiwar da Allah Subhanahu wa Ta’ala ya hore masa. Domin sun so Sarki Sanusi II ne ya zama dan amshin shatar su, shi kuma yaki yarda da haka, shine suka kafa masa kahon zuka, suka fara hassadar sa, har suka kai ga yin abun da suka yi na zalunci!

Kuma sannan duk wadannan mutane da suke adawa da Sarki Sanusi II, duk magautan sa, idan an tara su aka tambaye su, shin menene laifin Sarki Sanusi II, wallahi za ka tarar da cewa babu wani takamammen abun da zasu iya fada cewa yayi masu.

Sannan ya kamata gwamna Ganduje da dukkanin ‘yan siyasar da ke da hannu a cikin abun da aka yiwa Sarki Sanusi II, su sani cewa mulkin su fa yana da iyaka, kuma zai kare, za’a wayi gari basu kan mulkin. Kuma wallahi su sani, sai sun girbi dukkanin abun da suka shuka. Kuma Ganduje ya sani, wallahi Tinubu ba zai iya kare shi daga girbar dukkan abun da ya shuka ba. Ba dai duniya ce ba? Ina rokon Allah ya bamu rai da lafiya da nisan kwana, wallahi za mu sha kallo da izinin Allah!

Sannan yanzu don Allah ta yaya za’a yi talakan Najeriya ya yarda da irin wadannan ‘yan siyasar mayaudara? Su kuma ‘yan majalisar dokokin jihar Kano, da suka mayar da kan su ‘yan amshin shatar gwamna Ganduje, don Allah ta yaya za’a yi su dawo da mutuncin su a idon talakawan jihar Kano har su yarda da su, su amince masu, bayan sun zubar da mutuncin su, sun zama ‘yan amshin shatar gwamna Ganduje? Ina rokon Allah ya shirye su, kuma ya basu iko, su gano cewa fa duk abun da suke yi duniya tana kallon su, kuma bayan duniya akwai ranar hisabi.

Wassalamu Alaikum,

Dan uwanku, Imam Murtadha Muhammad Gusau ya rubuta. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.

Share.

game da Author