Babban Lauya mai kare hakkin jama’a, Femi Falana, ya aika wa Kwamitin Binciken Ibrahim Magu, wanda Ayo Salami ke shugabanci cewa, ana kitsa wa Magu shaidar-zur ta hanyar kulla masa zarge-zargen karya.
Falana ya ce akwai wasu ‘yan kasar Faransa biyu tare da wani lauya da Magu ya taba gurfanarwa a kotu, tare da tsare su a kurkuku cikin 2015.
An kulle Gnahouse Nazaire da Senoue Modeste tare da lauyan su mai suna Ferdinand Egede, bisa zargin yin fojare na takardun kamfanin Rana Prestige Industries Limited, da suka ce sa hannun na wata mata ce mai suna Rachidatou Abdou.
Sun yi fojare duk a cikin 2007, har da na Hukumar yi wa Kamfanoni Rajista, wato CAC.
Falana ya ce shi me know lauyan Rachidatou, wadda ta kai Turawan kara har aka kulle su a kurkuku, amma daga baya aka bayar da belin su. Sai dai a na shari’ar har yanzu.
A kan haka ne Falana ya ce ya gano Turawan sun rubuta wa Salami wasika cike da sharri ga Magu, wai su na neman Shugaban Kwamitin Bincike Ayo Salami ya kori shari’ar ta su.
Lauya Falana ya ce babban kuskure ne idan aka kori shari’ar, domin Turawan su na can yanzu haka a kasar Benin, a Kwatano su na bugun-kirjin cewa an kusa korar shari’ar da ake yi masu a Najeriya.
Sun ce sun samu kamun-kafa da Kwamitin Binciken Magu, sun rubuta wasikar da za ta sa a sallame su.
Ba wannan ne karo na farko da aka rika zargin ana yi wa binciken Magu ‘yar-burum-burum ba.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Babban Lauya Itse Sagay ya tofa wa Kwamitin Salami yawun barci.
Shugaban Kwamitin Mashawartan Shugaban Kasa Kan Rashawa, Farfesa Itsay Sagay, ya yi tofin rashin gamsuwa da yanayin mutanen da aka saka matsayin Mambobin Kwamitin Ayo Salami masu binciken zargin cin hanci da rashawa da karkatar da kudaden da ake yi wa tsohon shugaban rikon Hukumar EFCC, Ibrahim Magu.
Sagay ya ce bai taba ganin irin kakudubar bincike ba, inda za a rika kiran masu zargin Magu a bayan idon sa, sannan kuma a hana shi kwafen takardun bayanan binciken da ake yi masa, ballantana ya yi shirin kare kan sa kafin ya je gaban kwamitin bincike.
Rahotanni sun tabbatar Sagay ya ce, “a bisa dukkan alamu, dukkan ‘yan kwamitin kakaf din su Mai Shari’a Ayo Salami ne kadai adali a cikin su, wanda kuma ba wata boyayyar manufa ya je karewa ba.”
“Ina kalubakantar Kwamitin Ayo Salami, saboda yadda ya ke gayyatar masu zargin Magu ana karbar hujjojin da su ke bayarwa, ko kuma na ce zargi. Amma Kuma ba za a bai wa Magu kwafen zarge-zargen da ake yi masa ya gani ba, ballantana ya yi shirin kare kan sa.
“Sannan kuma baya ga rahotannin da mu ke karantawa, kwamitin cike ya ke fal daga DSS, Ma’aikatar Shari’a da sauran hukumomin tsaro. Alhali kuma su dai ne masu zargin sa din dai.
“Mai Shari’a Salami ne kadai wanda ba ya tare kowane bangaren masu zargin Magu.
“Kotun Koli ta taba tsine wa irin wannan kwamiti da aka taba kafawa a kan Gani Fawehinmi a cikin 1985. Domin ‘yan kwamitin su ne masu zargin sa.
“Amma na yi imani cewa Mai Girma Tsohon Mai Shari’a Ayo Salami ya na da nagarta da kima da darajar da ba zai taba yarda wasu ‘yan bankaura su yi amfani da rashin gaskiya su zubar masa da mutunci ba. Duk kuwa da irin rubabi-rubabin ‘yan kwamitin da ke cikin aikin binciken.”
Wata wasika ta bayyana wadda ke dauke da sunayen mutum bakwai da ke cikin kwamitin na Salami, masu binciken Magu.
Akwai Ayo Salami, tsohon shugaban Kotun Daukaka Kara ta Kasa (Arewa ta Tsakiya); Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Micheal Ogbezi (Kudu maso Kudu); wakilin Ma’ikatar Harkokin Shari’a, Muhammad Babadoko (Arewa ta Tsakiya); wakilin DSS, Hassan Abdulalhi (Arewa ta Tsakiya).
Sauran su ne Muhammdu Shamsuddeen daga Ofishin Akanta Janar ta Tarayya (Arewa maso Yamma); Douglas Egweme, daga Ofishin Sa-ido Kan Sirrikan Hada-,hadar Kudade (Kudu maso Gabas) da kuma Kazeem Atitebits, wanda shi ne Sakataren Kwamiti (Kudu maso Yamma).
Shi ma Magu ta hannun lauyan sa, ya sha kira da a fito fili ana yin tuhumar sa. Ya ce a kyale ‘yan kallo da ‘yan jarida su rika halarta.