Shugaban hukumar cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko ta kasa, NPHCDA, Faisal Shuaib ya bayyana cewa kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ita ce jigon yaki da cutar Shan-Inna a Najeriya.
Shuaib ya fadi haka da yake karbar bakuntar wakilin hukumar wakilin WHO a Najeriya a ofishin sa ranar Litini.
Ya ce Najeriya za ta samu shaidar rabuwa kwata-kwata da cutar shan-inna a Nahiyar Afrika a watan Agusta daga kungiyar WHO.
Hakan ya biyo bayan gamsuwa da Hukumar Yaki da Cutar Shan-Inna (POLIO) na kasashen Afrika (ARCC) ta yi game da kokarin kawar da cutar da gwamnatin kasar nan ta yi.
Shaidar rabuwa kwata-kwata da cutar shan-inna a Nahiyar Afrika
Idan ba a manta a watan Agusta 2016 ne cutar Shan Inna ta bullo a Najeriya bayan shekaru uku rabon da cutar ta bullo a kasar nan.
Bullowar cutar a shekarar 2016 ne ya hana Najeriya da Nahiyar Afrika samun shaidar rabuwa da cutar shan-inna.
Bayan haka Shuaib ya ce gwamnati ba za ta Yi kasa kasa ba wajen ganin ta kawar da cututtukan dake kama yara kanana musamman wadanda za a iya kawar da su ta hanyar yin rigakafi.
Mulombo ya jinjina kokarin da gwamnati ke yi wajen inganta fannin kiwon lafiya musamman cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a kasar nan.
Discussion about this post