‘Yan shia mazu zanga-zanga sun gwabza da jami’an tsaro a babban birnin tarayyan Najeriya, Abuja ranar Litini inda arangamar yayi sanadiyyar konewar wasu motoci na mutane da na gwamnati da dama.
Su dai ‘Yan shia sun fito zanga-zangar ci gaba da kira da suke yi ga gwamnati da ta saki shugaban su Ibrahim El-Zakzaky dake tsare tun a shekarar 2015.
Sun faro zanga-zangar ne daga mahadar Nitel inda suka dunguma zuwa Sakatariyar Abuja. A hanya suna Kabarbari suna cewa Allah ya kashe shugaban Amurka Trump, Allah ya kashe Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
A daidai sun Iso Sakatariyar ne sojoji suka nemi tsaida su amma hakan bai yiwu ba daga nan sai aka fara batakashi a tsakanin su.
‘Yan shi’an sun rika jejjefa wa motoci bamabaman kwalba da akayi da fetur ciki har da motocin hukumar bada agajin gaggawa ta kasa da wasu na mutane da dama.
Shugaban ‘yan shia da ya zanta da wakilin mu yace sun fito zanga-zangan su ne salin- alin kafin Sojoji suka far musu.
“Ba mu bane muka far wa sojoji, sune suka tsakale mu muna zanga-zangan lumanar mu.” Inji Yahaya.
Wannan ba shine bane na farko ba da ake arangama da jami’an tsaro ‘yan shia a Abuja. Ko a kwanakin baya an kashe ‘yan shia biyu sannan an harbi ‘yan sanda biyu a Majalisar kasa a wani zanga-zangar su.