Sakamakon binciken da kungiyar ‘Water Aid’ ta gudanar ya nuna cewa mutane miliyan 116 ne ke kantara bahaya a waje a Najeriya.
‘Water Aid’ ta sanar da wannan sakamako ne a taro da aka yi a Abuja.
Jami’ar kungiyar Evelyn Mere ta koka da cewa matsalar yin bahaya a waje ya karaɗe ko ina da ya haɗa da makarantu har da asibitoci.
“ Kashi 50 bisa 100 na makarantu da asibitoci a kasar nan basu da ingantattun dakunan bahaya sannan kashi 88 bisa 100 na makarantu da asibitoci basu da tsaftattacen ruwa.
Mere ta ce domin kawo ƙarshen wannan matsala ne ƙungiyar shirya shiri mai taken ‘VOTE4WASH’ wanda suka fara a lokacin zabe.
Shirin ya yi ƙoƙarin jawo hankalin ‘yan takara da ‘yan siyasa wajen daukan alkawarin kawo karshen matsalar dake tattare da yin bahaya a waje.
Mere ta ce burin yin haka shine domin karkato da hankalin gwamnati wajen zama a kan gaba a yaƙi da bahaya a waje da ake yi.
Bayan haka shugaban kungiyar Connected Development’ Hamzat Lawal a nashi tsokacin ya ce gaggauta hana yin bahaya a kasar nan ya zama dole ganin cewa rashin yin haka zai iya sa gwamnati yin asarar Naira biliyan 1.7 duk shekara.
“Sakamakon bincike ya nuna cewa kasar India ce kasar da ta fi kowace kasa matsalar yin bahaya a waje.
Ƙungiyar ‘Water Aid’ ta fara aiki a Najeriya ne a 1995 kuma tun a wancan lokaci take tallafa wa mutane kan hanyoyin tsaftace muhalli.
Discussion about this post