‘RIKICIN MAKIYAYA’: Alaafin na Oyo ya gargadi Buhari a kan ‘daukar fansar Yarabawa’

0

Alaafin na Oyo, Lamidi Adeyemi, ya yi gargadin cewa kabilar Yarabawa fa za ta iya fantsama fafutikar kare kan ta daga abin da ya kira “kara yawan fitinan makiyaya” kasancewa jami’an tsaron Najeriya “sun kasa yin komai” a kan matsalar.

Adeyemi ya yi wannan kakkausan furucin ne a cikin wata wasika da ya rubuta wa Shugaba Muhammadu Buhari, wadda ya rada wa suna: “Matsayin Yarabawa a Katankatar Najeriya.”

A cikin wasikar dai ya fito karara ya nuna damuwar sa a kan batun rashin tsaro a Najeriya.

Sai dai kuma ya fi nuna damuwar sa a kana bin da ya ce ke faruwa a yanzu a Ynakin Kudu Maso Yamma, inda shi ne Jihohin da suka kunshi kabilun Yarabawa.

“Na damu kwarai da halin rashin tsaron da kasar nan ke ciki. Amma kuma na fi damuwa da halin da jihohin yankin Yarabawa ke ciki, har da jihohin Edo, Kwara da Kogi. A kullum mu na fama da matsalar Fulani masu tare tare manyan titina su na garkuwa da kuma kashe mutane.

Alaafin ya yi magana ne bayan kisan Funke Olakunrin, ‘yar shugaban Kungiyar Gurguzun Yarabawa Zalla, wato Afenifere, wadda aka dora alhakin kisan ta a kan Fulani makiyaya.

Sai dai kuma har yau ‘yan sanda ba su bayyana ko su wa ne suka yi kisan ba.

“ Maganar da kuma matsalar duk da ya ce a ke fama da ita a kan hanyar Owo, Akure, Ilesa/Ife-Ibadan ko hanyar Ibarapa da Ijebu na Jihar Ogun.”

Daga nan sai ya dora laifin a kan Fulani makiyaya.

“Mun sha zama da shugabannin yanki, dattawa da kuma wadanda abin ya shafa, mu na tattauna munin hare-haren da Fulani ke yi gami da yi wa mata fyade, har a gaban mazajen su.”

“Wannan fa kenan, banda kuma lalata mana amfanin gona da kasa a wannan hali da ake fama da talaucin da ya yi katutu a fadin kasar nan.”

Share.

game da Author