Mai Shari’a ya hana Shekarau zuwa tarbar Buhari

0

Alkalin Babbar Kotun Tarayya, Lewis Alagana, ya hana tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau zuwa tarbar Shugaba Muhammadu Buhari a Kano.

Buhari ya je Kano ne a ci gaba da kamfen din yakin neman zaben 2015 da ya ke yi.

Ana tuhumar Shekarau da hannu wajen karbar naira miliyan 950 daga tsohuwar ministar fetur, Diezani Alison-Maduekwe.

An yi zargin cewa sun karbi kudaden ne domin kamfen din 2015.

Zaman kotun ke da wuya a yau Alhamis, sai lauyan Shekarau mai suna Jibrin Okutepa, ya mike ya nemi alkali ya dage karar domin Shekarau ya samu damar zuwa tarbar Buhari.

Alkali Alagana ya ki amincewa, ya nuna cewa wannan ba wani kwakwaran dalili da zai sa ya dage sauraren karar ba ne.

Bayan an jima, lauya Okutepa ya sake mikewa a karo na biyu, ya nemi a dage shari’ar. Ya na mai cewa:

“Ya Mai Girma Mai Shari’a, wanda na ke karewa dan siyasa ne, kuma ya na cikin wadanda Buhari zai mika wa tutar takarar sanata a yau wurin taro. Ina so a dage sauraren shari’ar nan, domin ya samu halarta.

Alkali ya ki amincewa, inda ya ce za a ci gaba da shari’ar a haka.

Nan take sai mai gabatar da kara daga Hukumar EFCC, wato Samuel Chinwe, ya gabatar da shaida na farko, wanda ya shaida wa kotu cewa ya samu rahoton sirri da ya tabbatar da cewa an narka wasu makudan kudade har naira biliyan 23 a wani asusu a Fidelity Bank, Legas.

Ya ce kudin daga Diezani, ministar fetur ta lokacin suka fito. Mai gabatar da shaida ya ce an kamfaci naira milyan 950 an bai wa Aminu Wali da Masur Muktar, jiga-jigan PDP na Kano a lokacin.

Ya ce an ba su kudaden a ranar 23 Ga Maris, 2015, ana saura kwana biyu zabe.

Mai Shari’a ya ce za a ci gaba da shari’ar a gobe Juma’a, 1 Ga Fabrairu.

Share.

game da Author