Daga hannun Ganduje da nayi ba shi da alaka da Yaki da Cin hanci da Rashawa da muka sa a gaba – Inji Buhari

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa don yana mara wa gwamnan Kano Abdullahi Ganduje baya shikenan kuma sai ace Yaki da Cin Hanci da gwamnatin sa ke yi ya zama shirme.

Fadar shugaban kasa ne ta fitar da wannan sanarwa da Garba Shehu ya saka wa hannu ta ce Yaki da cin Hanci Rashawa da gwamnati ke yi a yanzu da bam sannan goyon baya da Buhari yake yi wa Ganduje da bam.

sanarwar ta kara da cewa idan ba a manta ba Buhari ya zuwa yanzu ya tasa keyar wasu da dama da ake tuhuma da yin sama da fadi da kudaden gwamnati kuma wasun su ma har sun dade daure a kurkuku.

Game da Ganduje kuma sanarwar ta ce gwamnan yana da kariya da doka ta bashi da ba za a iya ci masa mutunci ba sannan haryanzu wannan zargi da ake masa na gaban kotu.

” A dokar Najeriya ba za a tabbatar da laifin ka ba har sai kotu ta yanke maka hukuncin haka. Ba zai yiwu ace haka kawai a afkawa mutum ba ba tare da an bi doka ba.

” Wannan gwamnati, gwamnati ce da take bin doka. Idan ba a manta ba da a ka tabbatar da zargi da ake ma shugaban hukumar Inshorar Lafiya ta kasa Yusuf Usman. Gwamnati ta umarce shi da ya tafi hutun dole domin bada dama a gudanar da bincike a ma’aikatar bisa zargin da ake yi masa.

Share.

game da Author