Ya tabbata dai cewa jam’iyyar APC ba ta da ‘yan takaran gwamna a jihohin Ribas da Zamfara.
Hakan ya bayyana ne a sunayen da hukumar zabe ta kasa ta fitar yau Alhamis inda ta jero sunayen duka ‘yan takarar gwamnoni da mataimakan su da za su fafata a zabe mai zuwa.
Idan ba a manta ba, ba da dadewa ba hukumar zabe ta sanar cewa jam’iyyar APC ba ta da ‘yan takara a jihohin Ribas da Zamfara a dalilin rashin gudanar da zaben fidda gwani da jam’iyyar ta gagara yi.
Kotun daukaka kara a Abuja ta tabbatar da haka a wani hukunci da ta yanke cewa ba ayi zaben fidda gwani ba na APC a jihohin.
Sai dai kuma a makon da ya gabata, kotu a garin Gusau ta yanke hukuncin hukumar zaben lallai ta amince da kwarya-kwaryar zaben fidda gwani da jam’iyyar na bangaren gwamnan jihar tayi.
Sanata Kabiru Marafa wanda shima dan takarar a lokacin ya bayyana cewa ba zai amince da wannan hukunci da kotun ta yanke ba. Sannan ya yaba wa kotun Abuja kan kin amincewa da wannan zabe da gwamnan jihar Yari yayi.
Marafa ya ce hakan da kotu ta yi yayi daidai.
Ga cikakken jerin sunayen ‘yan takaran gwamnonin jihohin kasar nan