Kungiyar likitocin Najeriya (NMA) ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta kafa mata hukumar kula da al’amarorin likitoci (MDCN) kafin nan da ranar 30 ga watan Satumba.
Shugaban kungiyar Francis Faduyile ya bayyana haka wa manema labarai a Abuja inda ya kara da cewa rashin kafa wannan hukuma zai ingiza su wurin daukan mummunar mataki.
Tun da gwamnati ta rushe tsohuwar hukumar (MDCN) shekaru uku da suka wuce, kuma a hakan bata kafa wata ba tun a lokacin kungiyar ta fada cikin mawuyacin hali, da ya shafi fannin kiwon lafiya na Kasar nan.
” A dalilin hakan muke kira ga gwamnati data gaggauta kafa wannan hukumar kafin nan da ranar 30 ga watan Satumba domin kuwa a shirya muke mu je kotu a kan haka.
Bayan haka Faduyile ya kuma ce kungiyar NMA na iya kokarin ta don ganin ta sasanta sabanin dake tsakanin ta da hadaddiyar kungiyar ma’aikatan jinya na kasa (JOHESU).
” Ya zama dole a sasanta mu musamman yadda aikin mu ya shafi kula da kiwon lafiyar mutane. Sannan a yanzu haka kotun hukunta laifukan masana’antun na kokarin ganin hakan ya faru.
A karshe Faduyile ya ce kungiyar NMA ta kafa dokar yin amfani da tambari wa kowani kwararren likita a kasar domin kawar da baragurbin ma’aikata daga fannin kiwon lafiya.
Ya kuma ce za su hada hannu da hukumar kula da al’amuran cibiyoyin kiwon lafiya na kasa don ganin gwamnati ta ware kashi daya bisa dari na kassafin kudin kasa domin inganta fannin kiwon lafiyar kasar.
Discussion about this post